1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Najeriya sun ceto mutum 241

Binta Aliyu Zurmi
May 29, 2020

Jami'an sojoji a Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane 241 daga hannun mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3cyEA
Nigeria 65 Menschen von Islamisten der Gruppe Boko Haram getötet
Hoto: AFP/A. Marte

Mai magana da yawun sojin kasar John Enenche ya ce daga cikin wadanda aka kubutar 136 yara ne sai mata 105, kuma an kubutar da su ne yayin wani sumame da sojoji suka kai kauyen Mudu da ke arewa maso yammacin jihar Borno a yakin da suka daura da 'yan ta'adda musamman ma 'yan kungiyar Boko Haram.

A wannan aiki jami'an tsaron sun yi nasarar kashe mayakan na Boko Haram goma sha biyu. Mutane 241 da aka kubutar da su daga hannun mayakan na karbar kulawa ta musamman daga jami'an kiwon lafiya.