Dakarun Kameru sun kwato dan kasar Jamus daga hannu Boko Haram | Labarai | DW | 21.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Kameru sun kwato dan kasar Jamus daga hannu Boko Haram

Gwamnatin kasar Kameru ta tabbatar da kubutar daga Bajamushen da Boko Haram ta yi garkuwa da shi na tsawon watanni shida

Gwamnatin Jamus ta tabbatar da cewa mahukuntan kasar Kameru sun kubutar da Bajamushen tsagerun Boko haram suka yi garkuwa da shi na watanni shida a Tarayyar Najeriya.

Fadar shugaban kasar Kameru ta bayyana cewa dakarun kasar da na kasashe da suke dasawa sun ceto Nitsch Eberhard Robert daga hannun 'yan Boko Haram a wata sanarwa ta wannan Laraba. Hargitsin tsagerun Boko Haram masu kaifin kishin addin Islama ya kai ga mutuwar fiye da mutane 14,000 akasari a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman