Dajin Falgore a halin yanzu | Amsoshin takardunku | DW | 19.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Dajin Falgore a halin yanzu

To shi dai wannan daji na Falgore yankin ne da ke da albarkatu daji hadi da dabbobi da bishiyu wanda ake ba shi kulawa ta musamman a Kudancin Kano a Arewacin Najeriya.

Bildergalerie Nashörner

Dabbobi na janyewa sannu a hankali saboda farauta

Wannan wuri da aka kebe na da tazara ta kilomita 150 daga birnin Kano, yankuna na shi na cikin kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa da Sumaila. Ya kuma yi iyaka tsakanin jihar ta Kano da jihohin Kaduna da Bauchi. Ya mamayi fadin kasa na murabba'in kilomita 1000 ko da yake ya zuwa yau ya ragu zuwa sama da murabba'in kilomita 800, ga Kogin Kano da ya ratsa ta cikinsa.

Symbolbild -Safari

Ziyarar irin wadannan gandun daji na neman zama tarihi saboda ta'addanci

Cikin tsarin yankunan yanayi na kasa da shuke-shuke da aka rarraba kasar Najeriya. Dajin na Falgore ya fada a Arewaci cikin yankin da ake kira Guinea Savanna a Turance.

Shi dai wannan gandun daji da ya faro da sunan Dajin Kogin Kano yanzu ake kira da suna Dajin Falgore ya samu tattali da bunkasa tun lokacin Turawan mulkin mallaka a shekarun 1940, ya kuma samu tattali da bunkasa ta musamman a shekarun 1960.

Karte Nigeria Kano Dakasoye

Dajin Falgore a Kudanci na Kano yake

Babban buri da ake da shi dai shi ne yadda za a killace dukkanin wasu dabbobi da ma yanayi shuke-shuke da kogi da sauran abubuwa da Allah ya halitta a wannan yanki. Ko da yake ya zuwa yanzu an samu koma baya na wasu tsirrai saboda sare bishiya da ma farautar dabbobi kamar gwanki da zaki da damusa da dai sauransu sun ragu sosai, wasu sun yi hijira zuwa Yankari da sauran wurare.

A wannan wuri ruwan na Kogin Kano da ke ratsawa gandun dajin hakan na sanyawa ruwan ya zama yana da tsafta, ka gan shi garai-garai misali idan ka kalli Tiga Dam da ruwan da ya shiga cikinsa ya ratsa gandun dajin ba kamar na Chalawa ba da bai ratsa gandun daji ba ya kasance yana da dauda da rairayi.