1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cyprus ta amince mata su zubar da ciki

Mouhamadou Awal Balarabe
March 30, 2018

Shekaru da dama bayan muhawara tsakanin shugabannin addini da masu neman sauyi, 'yan majalisar dokokin Cyprus sun amince da dokar da ke bai wa mata damar zubar da ciki matikarbai zarta wata uku ba.

https://p.dw.com/p/2vGSs
Indonesien Frauenhaus für uneheliche Schwangerschaften und Abtreibungen in Jakarta
Hoto: Monique Rijkers

Majalisar dokokin kasar Cyprus ko Chypre ta sassauta dokar da ke haramta wa matan kasar zubar da jiki ba tare da wani kwakwaran dalili ba, shekaru da dama bayan muhawara kan wannan batu a kasar da ke cikin kungiyar tarayyar Turai. 'Yan majalisa 33 ne suka yi na'am da kwaskwarimar da aka yi wa dokar zubar da cikin yayin da takwas suka kada kuri'ar kin amincewa, sauran biyar kuma suka yi rowar kuri'unsu.

Wannan sabuwar dokar tana bai wa matan Cyprus ko Chypre damar zubar da ciki bisa taimakon likita matikar bai fi wata uku ba . sannan kuma matan da aka yi wa fyade na da damar zubda cikin matikar bai kai wata biyr ba. Babu dai alkaluma kan yawan mata da ke zubar da ciki ta bayan fage a Cyprus ko Chypre, amma kuma an dade ana muhawara  akan wannan batu kafin a aiwatar da shi saboda karfin fada a ji da shugabannin addini ke da shi a kasar.