Cutar Corona na kara kamari a Saudiyya | Labarai | DW | 19.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Corona na kara kamari a Saudiyya

Hukumomin kiwon lafiya na kasar ta Saudiyya sun ce an samu sabbin kamuwa da cutar ta matsalar nunfashi guda 50 a cikin wannan wata na Agusta kadai.

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Saudiyya sun bada sanarwar samu karin wasu mutane 50 da suka kamu da cutar matsalar nunfashi ta Corona a kasar a cikin wannan wata na Ogusta kadai. Hukumomin kasar ta Saudiyya sun ce a ranar Larabar jiya kadai an samu mutane 10 da suka kamu da wannan cuta. Yaduwar wannan cuta ta Corona dai ya zo ne a daidai lokacin da kasar ta Saudiyya ke shirin soma karbar bakunci miliyoyin maniyata da za su je domin sabke faralin shekarar bana.

A shekara ta 2012 ne dai wannan cutar matsalar nunfashi mai saurin kisa ta Corona ta bayyana a kasar ta Saudiyya inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Mutane kimanin 800 ne wannan cuta ta hallaka a duniya baki daya tun bayan bullowarta ta farko a shekara ta 2002.