Covid-19: Saudiyya ta bude masallatai | Labarai | DW | 04.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Covid-19: Saudiyya ta bude masallatai

A wannan Lahadi kasar Saudiyya ta bude masallatan kasar a karon farko cikin watanni biyu.


Wannan kasa da ke zama cibiyar addinin musulumci ta rufe masallatan kasar a wani mataki na kare kai daga bazuwar annobar coronavirus. Duk da daukar wannan mataki dai kasar ta samu akalla mutum 83,000 da suka kamu da cutar. A cikin wannan adadi mutum 480 cutar ta yi ajalinsu.


''Ina ji a jikina cewa rahamar Allah ta sauka. Bayan mun kwashe wani lokaci muna kiran sallah don mutane su yi sallah a gidajensu, yau ga shi mun wayi gari mun kira sallah jama'a sun zo dakin Allah'' inji mai kiran sallah a kasar

To sai dai an saya dokar duk wanda zai je masallaci ya sanya takunkumi, ya kuma yi guzurin tabarmar da zai yi sallah a kanta. An kuma bukaci jama'a su rinka yin alwala daga gidajensu, sannan babu hada diga-digi a wurin sallah. Kazalika hukumomi sun haramta wa kananan yara da tsofaffi da kuma masu wasu cututtuka zuwa masallatan.


Duk da wannan sassaucin da aka fara samu a wannan Lahadi dai, babu wasu alamu da ke nuna cewa hukumomin Saudiyya za su bude kofa a ci gaba da Umrah da aikin Hajji a kwanaki masu zuwa.