COVID-19: Najeriya ta ki maganin Madagaska | Siyasa | DW | 03.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

COVID-19: Najeriya ta ki maganin Madagaska

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa maganin cutar COVID-19 da Madagaska ta ba ta, ba komai ba ne illa sinadarin maganin zazzabin cizon sauro, a dangane da haka ba za ta yi aiki da shi ba.

Guinea-Bissau Coronavirus Tee aus Madagaskar (DW/B. Darame)

Maganin coronavirus daga kasar Madagaska

Najeriyar dai ta dauki lokaci mai tsawo tana bincike a kan maganin da kasar Madagaskar ta bai wa kasar kyauta domin shawo kan cutar sarkewar numfashin ta COVID-19, inda bayan bincike na kimiyya aka fitar da sakamako na sinadaran da ke cikin magani da aka ce yana cike na sinadarai na Tazargade. Tun a ranar 16 ga watan Mayun wannan shekarar ne dai, Najeriya ta karbi maganin cutar coronavirus din daga kasar Madagaskar, inda kuma nan take shugaban kasar ya yi alakwarin za a gudanar da bincike na kimiyya.

Tuni dai 'yan Najeriyar da suka sa ran samun sauki ta hanyar kokarin da ake ganin Madagaskar ta yi, suka fara mayar da martani a kan sakamakon binciken kimiyyar da aka gudanar din. A yanzu dai  kallo ya sake komawa sama musamman ga kasashen Afirka, na su jajirce domin nemo maganin COVID-19 din, ba wai zura idanu na zaman tsammanin samun mafita daga kasashen da suka ci gaba ba, duk kuwa da cewa  fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar a Afrika sun warke.

Sauti da bidiyo akan labarin