1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka kamu da coronavirus a Indiya sun haura miliyan

Abdoulaye Mamane Amadou
July 17, 2020

Indiya ta zarta mutum fiye da miliyan daya da aka tabbatar da sun kamu da annobar Covid-19 a cewar hukumomin kiwon lafiya lamarin da yasa kasar ta zama ta uku a duniya da suka fi wadanda suka kamu da Covid-19.

https://p.dw.com/p/3fSOy
Indien Coronavirus
Hoto: Reuters/F. Mascarenhas

Rahotanni daga wasu yankunan kasar sun nuna cewa an shiga daukar muhimman matakan sake dakile yaduwar annobar karo na biyu, inda ake daukar matakan kakaba dokar kulle da takaita zirga-zirgar jama'a.

A yanzu dai Indiya ita ce kasa ta uku da tafi yawan wadanda suka fi kamuwa a duniya biyo bayan Amirka da Brazil. A yanzu alkaluma na nuni da cewa wadanda suka mutu sun kai fiye da dubu 25.600 biyo bayan sun kamu da cutar coronavirus.