Covid-19: Adadin wadanda suka mutu sun karu | Labarai | DW | 07.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Covid-19: Adadin wadanda suka mutu sun karu

Adadin wadanda suka hallaka sakamakon kamuwa da cutar corona a duniya sun haura mutun 263.790 kamar yadda wata kididdigar da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ke fitarwa kowace rana

Har yanzu dai kasar Amirka ce ke kan gaba daga cikin wadanda mutane suka fi mutuwa da cutar, inda take da mutun fiye da dubu 77 da suka kwanta dama, a yayin da Birtaniya ke biye mata da mamata fiye da dubu 30. Italiya na da dubu 29 da 684, sai Spain mai fiye da dubu 26, a yayin da Faransa ke da mamata 25 da 809.

Har yanzu nahiyar Afirka ce ke da kaso mafi karanta na wadanda rayukansu suka salwanta inda kididdigar ta ce ya zuwa yanzu mutun 2.007 ne suka mutu daga cikin akalla dubu 51 da 569 da aka hakikance sun kamu da cutar.