Coronavirus na ci gaba da shiga kasashen Afirka | Labarai | DW | 03.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Coronavirus na ci gaba da shiga kasashen Afirka

Kasar Moroko, ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar cornonavirus, kasar da ta kasance ta baya-bayan nan da cutar ta bulla a cikinta a nahiyar Afirka.

Hukumomi a Morokon sun ce mutumin da ya nuna alamun cutar ya shiga kasar ne daga Italiya, kuma yana kwance a wani asibiti da ke birnin Casablanca.

Morokon na sanar da hakan ne kuwa sa'o'i kalilan bayan kasar Tunisiya ta sanar da samun wani wanda shi ma ya koma kasar daga Italiya da ya harbu da ita.

Ita ma kasar Senegal ta sanar da samun wani Bafaranshe mazaunin kasar da gwaji ya tabbatar yana dauke da cutar, kamar yadda ministan lafiya, Abdoulaye Diouf Sarr, ya bayyana.

Akalla dai akwai kasashen Afirka 11 da aka tabbatar da bullar coronar a cikinsu a yanzu.

Rahotanni daga kasar Japan ma dai sun tabbatar da samun mutum na farko a yau Talata da ke dauke da sabuwar matsalar ta lafiya.