Coronavirus: An tsawaita dokar kulle a Kano | Labarai | DW | 18.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Coronavirus: An tsawaita dokar kulle a Kano

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar corona a Najeriya ta bakin shugabanta Boss Mustapha a yau Litinin ya sanar da tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihar Kano da karin makwanni biyu.

Da yake jawabi ga manema labarai sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce har wa yau dokar saka tazara a tsakanin al'umma da ma ta zirga-zirga tsakanin jihoji su ma duk an kara musu makwanni biyu. Boss Mustapha ya kara da cewar wannan yaki da ake da cutar Covid 19 ba abu ne da zai kare rana daya ba, a sabili da haka duk jihar da aka samu karuwar cutar za a iya saka mata wannan doka da Kano ke ciki.

Jihar Kano dai na zama ta biyu a fadin Najeriya da alkalumman wadanda ke dauke da cukar suka haura mutum dari takwas kana sama da mutum 35 su ka rigamu gidan gaskiya.