1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ciyar da dalibai a Nijar albarkacin Azumi

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
April 21, 2022

Musulmi a Nijar, sun dukufa wajen neman falalar watan Azumi wajen ciyar da dalibai a jami'a. Wannan al'ada ta ciyarwa dai na taimaka wa dalibai da dama wadanda ke madalla da samun haka.

https://p.dw.com/p/4AFLV

Al’ummar Musulmin kasar Nijar na ci gaba da bin sauran takwarorinsu Musulmi na duniya wajen gudanar da Azumin watan Ramadan da ke zama daya daga cikin shika-shikan muslunci. Kuma lokacin buda baki na zama lokaci mafi mahimmanci ga mai Azumi. Sai dai al’adar buda baki na shan bam-bam daga wata kasa zuwa wata ko daga wasu iyalai zu wasu.