Ci gaba da hare-hare a Maiduguri | Labarai | DW | 02.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da hare-hare a Maiduguri

A Najeriya ana ci gaba da fuskantar hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar da ke zaman tushen kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar.

Hare-haren Boko Haram a Najeriya

Hare-haren Boko Haram a Najeriya

Wani bam da ya tashi a wata kasuwar dabbobi a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya hallaka mutane da dama yayin da wasu kuma suka jikata. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa da misalin karfe daya na rana ne suka ji kara mai karfi nan take kuma mutane suka ranta a na kare. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan yadda al'amarin ya faru kana babu masananiya kan adadin wadanda harin bam ya rutsa da su. Wani kwamandan matasan nan da aka fi sani da Civilian JTF ya tabbatar wa da wakilinmu na Gombe Al-Amin Suleiman Muhammad da tashin bam din.