1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi ta musanta zargin kashe masunta a Tafkin Chadi

May 15, 2026

Gwamnatin Chadi ta yi watsi da zargin kashe fararen hula a farmakin da sojoji suka kai a yankin Tafkin Chadi da zummar murkushe mayakan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/5DoTp
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Déby Itno
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Déby ItnoHoto: Mikhail Metzel/dpa/AP/picture alliance

Mutane da dama suka mutu sakamakon mabambantan hare-hare da dakarun sojin Najeriya da kuma na Chadi suka kai a makon da ya gabata. Wasu mazauna yankin Tafkin Chadi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sojojin Chadi sun halaka masunta sama da 40 a yankin.

Karin bayani:MDD ta ce a bincika kashe-kashen jama'a a Najeriya da Chadi

Ministan sadarwa na kasar Chadi Gassim Cherif Mahamat bayyana cewa an kitsa labarin ne domin a ragewa dakarun kasarsa karsashi, a kokarinsu na murkushe mayakan Boko Haram. Ministan ya kuma kara da cewa za su kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamari kan zargin kashe fararen hula a yankin Tafkin Chadi.