Chadi da Nijar na fatattakar Boko Haram | Siyasa | DW | 09.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Chadi da Nijar na fatattakar Boko Haram

Haɗin gwiwar sojojin ƙasashen da ke yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace garin Damasak da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Tschad Militär

Sojojin ƙasar Chadi

Tun da safiyar jiya ne dai shaidu daga garuruwan Diffa da Bosso masu iyaka da Najeriya suka tabbatar da jin ɓarin wuta na bindigogi a kan iyakokin ƙasashen, kafin daga bisani a samu labarin cewar haɗin gwiwar sojojin ne ya kutsa Najeriya.


Manazarta na bayyana ra'ayoyin cewar ana daf da kawo ƙarshen Boko Haram

Tschad Militär

Sojojin ƙasar Chadi

Masharhanta sun fara bayyana matakin da ƙasashen suka ɗauka da cewar shi ne mafi kyau domin idan ba haka ba kogo yana iya juyewa da mujiya,Dokta Isufu Yahaya malami ne a jami’ar Yamai kuma mai yin sharhi a kan al'amuran tsaro.
'' Yanzu na ke ganin yaƙi ya fara tun da an tafi an bi 'yan Boko Harama har inda suke ɓoyewa a Najeriya kuma ana ganin,yin hakkan wani babban yunƙuri ne wanda zai karya lagon 'yan tawayen waɗanda suka daɗe suna kai hare-hare ga jama'a.''

Akwai alamun cewar ana daf da kawo ƙarshen Boko Haram

Tschad Militär Soldaten

Sojojin ƙasar Chadi

Wannan dai shi ne karon farko da haɗin gwiwar sojojin na Chadi da Nijar suka kai harin bazata a sanssanin Boko Haram ɗin tare da samun nasara ƙwace garin Damasak.
Farfesa Ado Mahaman shugaban jami’ar Tahoua da ke a Jamhuriyar Nijar ya ce wannan yunƙuri wata babbar nasara ce. ''Idan har ba su gama ƙarfi da ƙarfe ba suka yi wa Boko Haram tarayya to Boko Haram za ta zama wata wutar daji da za addabi duniya baki ɗaya.''

Kafin dai ƙasashen su kutsa a Najeriyar a wani sabon saƙon bidiyio da ya wallafa shugaban Ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce ungiyarsa ta miƙa wuya ga Ƙungiyar IS.Abin da wasu manazartan ke ganin wani babban ƙalubale da ke a gaban ƙasashen da ke yaƙi da Boko Haram.

Sauti da bidiyo akan labarin