Ceton masu shaye-shaye a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 28.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Ceton masu shaye-shaye a Najeriya

A Jihar Kanon Najeriya wani mutum mai suna Dr Yakubu Maigida Kachako ya samar da wata cibiyar kyautata halayya ta matasan da suka samun kansu cikin lamarin shaye-shaye na miyyagun kwayoyi.

Za a iya cewar  cewar wannan shi ne karo na farko da aka girka wata cibiyar kyautata halayya ga matasa ‘yan maye a jihar Kanon Najeriyar, wacce ke samar da horon guje- guje da tsalle- tsalle domin dauke hankulan matasan gami da gudanar da bitoci baya ga tallafin shiga makaratu don samun makoma ta gari ga matasan a nan gaba. Dr,Yakubu Maigida Kachako shi ne jagoran wannan cibiya: "To, abin da ya faru ni ina cikin Hukumar Hisba bayan cibiyar da nake yi lokacin da ke cikin hukumar ina ganin yadda ake futa a je a yi kame a kamo yara masu shaye-shaye da sauransu idan ka duba sai ka ga mafiya yawa s marayau ne wasu kuma ya'yan marasa karfi ne. Kuma babban burin da k a gabana shi ne na taimaka wa wadannnan matasa su sami kyakyawar rayuwa.”

 

Sauti da bidiyo akan labarin