1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Cece-kuce kan raba gari da kochin Super Eagles Jose Peseiro

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
March 4, 2024

Mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya Jose Perseiro ya raba gari da Super Eagles bayan da kwantiraginsa ta kare. Ita kuwa Bayer Leverkusen ta ci gaba da zama a saman teburin gasar Bundesliga ta Jamus.

https://p.dw.com/p/4d8nm
Jose Vitor Dos Santos Peseiro ya kai Super Eagles har matakin karshe a Afcon
Jose Vitor Dos Santos Peseiro ya kai Super Eagles har matakin karshe a AfconHoto: Segun Ogunfeyitimi/Shengolpixs/IMAGO

A Najeriya takadama ta kuno kai bayan sanar da ajiye aikin da coach Jose Peseiro na kungiyar Super Eagles ya yi. domin ‘yan kwanakin kalilan bayan nasarar da matakin ya samu kaiwa ga wasan karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka da ta gudana a Côte d ' Ivoire.

Leverkusen na ci gaba da jan zarenta a Bundesliga

Bayer Leverkusen ta ci gaba da rike kambunta na saman teburin Bundesliga tare da yi wa Bayern tazara da maki 10, bayan da ta lallasa takwararta FC Cologne da ci 2-0 a karshen mako. Bayern Munich ta gaza kai bantenta a gidan Freiburg, inda suka tashi wasa 2-2. Augsburg ta bi Darmstatd har gida ta caskara ta da ci 6-0, yayin da aka tashi wasa kunne doki 1-1 tsakanin Mainz da Borussia Mönchengladbach. Ita kuwa Borussia Dortmund ta bi Union Berlin ne har gida ta kuma lallasa ta da ci 2-0, kana Frankfurt ta yi nasara a gidan Heidenheim da ci 2-1.

Leverkusen ta bi takwararta Cologne har gida kuna ta doke ta da ci 2-0
Leverkusen ta bi takwararta Cologne har gida kuna ta doke ta da ci 2-0Hoto: Christian Schulze/Nordphoto/IMAGO

Haka abin ya ke a wasa tsakanin Hoffenheim da Werde Bremen, inda aka tashi wasa Hoffenheim na da ci biyu Bremen na da ci daya. Sai kuma wasa tsakanin Bochum da Lepzig da sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye. Sai dai murnar Bochum da ke wasa a gida ba ta dore ba, domin kuwa a mintuna na 30 Lepzig ta farke wannan kwallo kana da aka dawo hutun rabin lokaci ta kara wa Bochum din kwallaye uku, abin da ya sanya aka tashi Bochum na da ci daya Leipzig na da hudu. Har yanzu dai Leverkussen ke saman tebur da maki 64 sai Bayern a matsayi na biyu da maki 54 yayin da Stuttgart ke a matsayi na uku da maki 50.

Yadda ta kaya a gasar kwlalon Spain da Ingila 

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ga samu ta ga rashi, yayin da a karon farko tun bayan da dan wasanta Vinicius Jr ya fuskanci kalaman wariyar launin fata a filin wasa na Mestalla a watan Mayun 2023 ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Valencia. An dai tashi wasa biyu da biyu, sai dai alkalin wasan ya busa tashi a daidai lokacin da Real Madrid ta kusa ziua kwallo na uku a raga yayin da kwallon ke sama, abin da ya sanya dan wasanta Jude Belingham yin korafi shi kuma alkalin wasan ya ba shi jan kati duk kuwa da cewa ya busa tashi. Har yanzu dai Real Madrid din ce ke saman tebur da maki 66 yayin da Girona ke biye mata a matzsayi na biyu da maki 59 sai kuma Barcelona a matasayi na uku da maki 58.

Lokacin karawa tsakanin Chelsea da Liverpool
Lokacin karawa tsakanin Chelsea da LiverpoolHoto: Hannah Mckay/REUTERS

A gasar Premier League ta kasar Ingila kuwa, har yanzu Liverpool ke saman tebur da maki 63 bayan wasanni 27, yayin da Manchester City ke a matsayi na biyu da maki 62 ita ma bayan wasanni 27 kana Arsenal ke a matsayi na uku da maki 58 a wasanni 26.

Dambe da guje-guje sun dauki hankali a karshen mako

A karshe dai, an wanke dan wasan damben kasar Birtaniya Dillian Whyte da soso da sabulu, bayan da aka gano cewa gurbatattun magunguna kara kuzari gabanin fafatwarasu da takwaransa Anthony Joshua a bara, kamar yadda gwaji ya nuna. Whyte ya shiga halin tsaka mai wuya, bayan da gwajin kwayoyi da ya yi na sa-kai ya janyo masa soke karawar da zai yi da Joshua a watan Agustan bara. Sai dai bayan gudanar da bincike, an gano cewa ya sha wasu magunguna na kara lafiya ne da suka gurbata, koda yake har yanzu babu karin haske. Da yake zantawa da gidan talabijin na Sky, mai shekaru 35 a duniya, Whyte ya ce "ransa ya baci kuma bai ji dadi ba" kan zargin da aka yi masa, amma yana takaicin damar gwabzawa da Anthony Joshua da ya rasa.

'Yar gudun fanfalaki Femke Bol ta zama ta daya a duniya
'Yar gudun fanfalaki Femke Bol ta zama ta daya a duniyaHoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Tsohuwar 'yar gudun fanfalaki ta kasar Holland Femke Bol ta sake kafa sabon tarihi a tseren mita 400, yayin da Josh Kerr na Birtaniya ya yi nasara a tseren mita 300 a bangaren maza a gasar cin kofin tseren duniya na world indoor athletics. Mai shekaru 24 a duniya, Bol ta karkare gudun a dakika 49 da digo 17 kasa da tarihin da ta kafa makonni biyun da suka gabata a gasar cin kofin tsere na kasar Holland da ta kammala tseren mita 400 a dakika 49 da digo 24.