Cece-kuce kan haramta zanga-zanga a Abuja | Siyasa | DW | 18.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cece-kuce kan haramta zanga-zanga a Abuja

Matakin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dauka na hana masu zanga-zanga tsayawa a dandalin ‘yanci na birnin Abuja ya haifar da mayar da martani duba da halarcin da tsarin mulki ya bai wa al'umma a kan wannan batu.

'Yan sanda sun toshe masu zanga-zangar da suka fita domin yin gangami a wuri guda a birnin Abuja  kasa da sa'o’i 24 bayan da sifeto janar na rundunar ‘yan sanda ya fitar da sabuwar ka'ida da ta haramta zanga-zanga a kan tituna kowace iri ce. Sai dai tuni kungiyoyi kare hakkin jama’a sun nuna rashin amincewa da ma dacewar wannan haramci daga ‘yan sandan.

Kakakin rundunar 'yan sanda Franka Mba ta bayyana cewa irin yadda masu zanga-zanga ke kawo cikas da ma lalata dukiyar jama’a ya sanya su daukan wannan mataki, domin a makonin nan an yi ta artabu da ‘yan Shi’a a birnin. Sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a tsakanin ‘yan Najeriya a kan wannan batu, sanin cewa zanga-zanga na zama makami da talaka ke amfani da shi wajen nuna korafinsa a tsari na dimukuradiyya.

A yayin da wasu kungiyoyi ke shirin kalubalantar lamarin a gaban kotu, masharhanta na bayyana bukatar sake lalle a daukacin lamarin da masu zanga-zangar ke kallon matakin da za a iya dangantawa da a dokesu a hanasu kuka.

Sauti da bidiyo akan labarin