1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:Bukatar sauya kudin CFA

Salissou Boukari AH
January 30, 2019

Yanzu haka a kasashe da dama na Afirka masu amfani da kudin CFA ana ci gaba da nuna bukatar kawo sauyi don maye gurbin kudin na CFA, furci na baya-baya nan ya fito ne daga wani jami'in gwamnatin Nijar.

https://p.dw.com/p/3CSYg
Westafrika CFA-Franc BEAC
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A baya dai mataimakin shugaban gwamnatin kasar Italiya ne ya farfado da wannan batu na kudin CFA, inda ya ce wannan kudi na kasashen Afirka renon Faransa, ya kansance wani babban kalubale ga tattalin arzikin Afirka. Ministan kudin na Nijar Hassoumi Massaoudou dai ya jinjina wa kudin na CFA, inda ya ce yana taimaka wa wajan samun kwanciyar hankali a fuskar saye da sayarwa, sannan alakarsa da kudin Euro wannan ba wani sabon abu ne ba domin abin da yake da mahimmanci ita ce siyasar kudin da aka samar da za ta ba da damar bunkasa tattalin arziki da kuma ci gaba nan zuwa wani lokaci.

Mahamadou Issoufou Premierminister von Niger
Hoto: picture alliance/S. Minkoff

Shugaban Nijar ya taba tattauna batun na canza kudin CFA da tsohon shugaban kasar Benin

Sai dai duk da wannan tsokaci da ministan na kudi na Nijar ya yi na cewa bai ga laifi ga kudaden na CFA ba, ta shafinsa na Facebook, ofishin minista mai magana da yawun gwamnatin na Jamhuriyar Nijar ya shaida cewar shugaban kasa Issoufou Mahamdou ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Bernin Nicephore Soglo, wanda shi ma ya tabbatar da mahimmancin samun kudin na bai daya da kasashen ke yunkurin yi nan zuwa wani dan lokaci.