1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CDU ta Merkel ta sha kaye a zaben jihohi

March 15, 2021

Jam'iyyar Angela Merkel ta yi asarar kujeru a majalisun dokokin na wasu jihohi Jamus a zaben yankuna da aka gudanar, wanda ya bai wa jam'iyyun Greens da SPD damar lashewa a Baden-Württemberg da Rhineland-Palatinate.

https://p.dw.com/p/3qdMv
Deutschland Landtagswahl Baden-Württemberg | Winfried Kretschmann
Hoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

Jam'iyya mai mulki ta CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da abokiyar kawancenta ta CSU sun kwashi kashinsu a hannu a wasu zabubbukan jihohi biyu da aka gudanar a jiya Lahadi (14.02.2021). A jihar Baden-Württemberg dai, Jam'iyyar Greens ta lashe zaben, yayin da a jihar Rhineland-Palatinate kuma Jam'iyyar SPD ta samu sabon wa'adi.

Sai dai ana danganta wannan kayen da jam'iyyar ta sha da murabus din da wasu 'yan majalisar tarayya na jam'iyyar suka yi sakamakon zargin su da aka yi da yin almundahana da kudaden sayen kayayyakin yaki da Corona.

Wannan na nufin cewa akwai jan aiki a gaban jam'iyyar mai mulki ta CDU wajen kara janyo hankulan 'yan kasar idan har tana son kai bantenta a babban zaben kasar da za a gudanar nan da 26 ga watan Satumba mai zuwa, inda za a zabi wanda zai maye gurbin Merkel.