Canza sunan Gwoza da Mubi na Najeriya | Labarai | DW | 06.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Canza sunan Gwoza da Mubi na Najeriya

Kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriya ta sauyawa garuruwan Gwoza da Mubi da a yanzu haka ke karkashin ikonta suna.

Wasu da suka samu nasarar teserewa daga wadan nan garuruwa sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a yanzu kungiyar ta Boko Haram ta canja sunan garin Gwoza da ke jihar Borno suna zuwa Darul Hikma yayin da ta canja sunan garin Mubi na jihar Adamawa zuwa Madinatul Islam. Kungiyar dai ta kwace garin na Gwoza ko kuma Darul Hikma kamar yadda ta ke kiransa a yanzu tun cikin watan Yulin da ya gabata yayin da ta kwace garin Mubi da ke zaman birni na biyu mafi girma a jihar Adamawa a wanda kuma take kira da Madinatul Islam a watan Oktoban da ya gabata. Idan ba a manta ba cikin wani faifen bidiyo da ya fito a watan Agustan da ya gabata, shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau, ya ayyana garin na Gwoza a matsayin wani bangare na daularsu da suka kafa da suka ce ta Musulunci ce. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram ne ke yin sintiri a kan hanyoyi a garin Gwoza ba tare da fuskantar kalubale daga jami'an tsaro ba. Garuruwan biyu dai dukkansu na yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriyar ne da ke fama da hare-haren Boko Haram din.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu