1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kawar da fatara a Najeriya

Uwais Abubakar Idris ZUD
May 20, 2022

Kwararru na taron nema wa Najeriya mafita dangane da talauci da rashin tsaron da ke addabar ta. Burin masu taron shi ne samar wa shugabannin Najeriya da za a zaba a badi alkiblar fitar da kasar daga talauci.

https://p.dw.com/p/4Becb
Nigeria Reis-Pyramide gegen die Hungersnot im Land
Hoto: Koula Sulaimon/AFP

A yayin taron, an yi kokarin gano bakin zare game da abubuwan da ke sanya tattalin arzikin Najeriyar fuskantar komabaya a Abuja, inda kwararru a fannin tattalin arzikin da ma siyasa suka gano sassa bakwai da dole ne a duba su. Bangarorin kuwa sun hada da; tsaro da samar da  kayan aiki da sahihin shugabanci.  

Cibiyar nazarin harkokin tattalin arziki da ta shirya zaman mai taken ''kalubalen da ke fuskantar Najeriya, in ba’a dau mataki a yanzu ba sai yaushe'' ta tsara shi a matsayin wata dabarar sama wa shugabanin da za’a zaba a 2023 alkiblar da ya kamata su dosa. 

Farfesa Osita Ogbu, kwararre a fannin tattalin arziki da ke jami’ar Najeriya ta Nsuka da ya gabatar da mukala a wurin taron ya ce ''idan ba a bunkasa tsarin yanayin aiki ta hanyar aiki tukuru ba, to babu yadda za a samu ci gaba.'' Farfesan ya ce wajibi ne shugabannin Najeriya su mayar da hankali ga bunkasa masana'antu domin samar da ci gaban kasar da al'ummarta ke fama da fatara.

Shamsudeen Abdullahi, wani kwararre a fanin tattalin arziki a Abuja na ganin duk shirin da za’a yi zai aiki ne kawai in an sauya tsarin da ake tafiyar da Najeriyar a yanzu domin ci gaban tattalin arzikinta. Sai dai Dr. Zayyanu Usman Malami a jami’ar Usman Dan Fodio, Sokoto, ya ce ‘yan kasa na da gagarumin aiki a gabansu don samun nasarar abin da aka tsara. 

Komabayan tattalin arziki da wannan taro ke dubawa na tayar da hankalin kwararru a daidai lokacin da Najeriyar ke shirin sabon zubi na shugabani bisa tsarin dimukuradiyya a badi.