Bukatar yafe bashi ga Najeriya da kasashe matalauta | BATUTUWA | DW | 08.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Bukatar yafe bashi ga Najeriya da kasashe matalauta

Gidauniyar Heinrich Böll ta Jamus ta yi kira ga manyan kasashen duniya su dauki matakin yafe wa Najeriya da sauran kasashe masu raunin tattalin arziki bashin da ake binsu.

Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria

Mai martaba tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

Mahalarta taro na gidauniyar Heinrich Böll da ya gudana ta kafar bidiyo, gaba daya sun yi ittifakin cewa basuka sun yi wa Najeriya daurin demon minti. Daga Naira Tiriliyan 12.6 da ake bin Najeriya a shekara ta 2015 kawo shekara ta 2019 bashin da ake bin kasar ya kai Naira Tiriliyan 27.1 Kazalika mahalarta taron na wannan alhamis na hasashen bashin da ake bin Najeriya zai karu zuwa Naira Tiriliyan 38.7 a wannan shekara. Gidanuiyar Heinrich Böll ta nemi a duba tsarin da ta kawo na neman manyan kasashen duniya su yafe wa kasashe irinsu Najeriya bashin da ke wuyansu, don babu alamu za su iya biya a cikin sauki musamman bayan da zuwan annobar corona ya kara dagula al'amura. To sai dai  a cewar Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya kuma tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi, daya daga cikin mutanen da suka yi bayani a wurin taron na bidiyo, duk da cewa yana goyon bayan tsarin yana da wani hanzari.

Heinrich Böll Stiftung | Nigeria Schulden Debatte

Mahalarta taron gidauniyar Heinrich Böll a Najeriya

''Nima na amince a yi wa Najeriya afuwar bashin da ake bin ta, amma kuma ya kamata mu gabatar wa duniya manufofin da za su nuna cewa lallai idan an yi mana afuwa nan da shekaru biyar ko 10  ba za mu sake komawa mu nemi a bamu wani rance ba.''

Bashin da Najeriya dai ta karba daga hukumomin kasa da kasa da kuma kamfanoni ya tilasta mata kashe kaso 83 cikin 100 na kudin da ta samu a shekarar da ta gabata a wurin biyan bashi, kuma duk da haka gwamnatin na ci gaba da hankoron karbo wasu basussukan domin tafiyar da gwamnati. Akan wannan Malam Sanusi Lamido Sanusi na cewa tsarin mulkin Najeriya na bukatar a gyara shi ta yadda koda an yafe wa Najeriya bashin da ake bin ta za ta samu tattalin arziki mai dorewa wanda zai hanata sake komawa kasashen duniya da 'yar murya, a kara mata rancen kudi.

''Ka dai ga shugababn kasa da mataimamkinsa, ga shi kuma tsarin mulki ya ce a samu minista daga kowace jiha, sannan ga 'yan majalisar tarayya guda 360 da sanatoci guda 109, kuma dukkaninsu an ba kowa damar ya dauki ma'aikata da za su yi masa aiki. Mun jefa kanmu cikin wani hali. To ka ga idan a matsayinka na mai bayar da rance ka ba kamfanin da galibin rancen da ka ba shi yake kashewa a kan jagororin kamfanin a maimakon kayan da ake sarrafawa, wannan bashi ba shi da amfani.''

Nigeria Sanusi Lamido Sanusi

Alhaji Sanusi Lamido Sanusi

Babbar shawarar da gidauniyar Heinrich Böll ta Jamus ta bayar dai ita ce idan har kasashe irinsu Najeriya suka samu zarafi aka yafe musu bashin da ake bin su to su mayar da hankalinsu wurin kyautata muhalli da samar da yanayin da muhalli zai kawo wa kasar kudin shigar da zai hana ta komawa 'yar gidajen jiya har bashi ya yi mata katutu. Jochen Luckscheiter shi ne shugaban gidanunyar ta Heinrich Böll a Najeriya.

"Tattaunawarmu ta tabbatar da cewa lallai Najeriya na bukatar a yafe mata basuka, amma kuma muna son a duba da kyau a aiwatar da manufofin da za su hana kasar komawa cin bashi nan da shekaru biyar ko goma. Akwai bukatar a nuna gaskiya dangane da basukan da aka karbo ko kuma aka yafewa kasar.''

A halin da ake ciki sassauci guda da manyan kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki na G20 suka yi shi ne na sanya kasashe matalauta dakatar da biyan bashin da ake bin su har zuwa wani dan lokaci, kuma har yanzu sauran kasashen da ba na G20 ba, basu nuna alamun za su yafe wa kasashe irinsu Najeriya dumbin kudade da ake bin su a saboda halin karayar tattalin arziki da dunyia ta shiga ba.

Sauti da bidiyo akan labarin