Bukatar sako ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 10.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar sako 'yan matan Chibok

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci 'yan kungiyar Boko Haram su sako 'yan matan nan 'yan makarantar sakandare da suka sace.

A watan Afrilun shekarar da ta gabata ta 2014 ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriya suka sace 'yan matan har sama da 200 a garin Chibok da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar.

A wani sabon faifayen bidiyo da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar a mako mai karewa, ya yi barazanar fadada hare-hare zuwa kasar Kamaru da ke makwabtaka da Najeriyar. Tuni dai Shugaba Paul Biya na Kamarun ya bukaci taimakon sojojin kasa da kasa domin taimakawa wajen fatattakar 'yan Boko Haram.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo