Bukatar dage zaben Najeriya da ke tafe | Siyasa | DW | 22.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukatar dage zaben Najeriya da ke tafe

Sambo Dasuki mai bada shawara ta musamman ga shugaba Jonathan ya ce hukumar ta INEC ta raba kati miliyan talatin yayin da miliyan talatin kuma ke hannunta.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega

Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya

An bukaci a dage zabukan da ake son yi a Najeriya a watan Fabrairu mai zuwa dan a bada dama sosai ga masu shirya zaben su shirya sosai wajen raba katinan zabe na din-din-din ga miliyoyin al'ummar kasar da suka cancanci kada kuri'a.

Mai bada shawara ta musamman ga shugaban Najeriyar kan lamuran tsaro ya bayyana haka a ranar Alhamis (22.01.2015).

Nigeria Wahlen 2011 Bild 3

Sambo Dasuki ya bayyana haka ne a wata tattanawa da aka yi da shi a cibiyar kula da tsare-tsaren kasashe ta Chatham House da ke birnin Landan. Ya ce tuni sun tattauna da shugaban hukumar zaben ta INEC wanda kuma ya ce tsaiko da bai wuce ka'idar doka ba yana da kyau:

"Wannan shi ne abinda mu ke bada shawara a wannan lokaci"

Wannan karo dai da ake son amfani da wannan kati na din-din-din na zama na farko da ake son amfani da kati mai kunshe da bayanai na sirri wanda ake so a yi amfani da shi dan kaucewa almundahna.

Dasuki ya ce hukumar INEC ita ke da alhaki ta nemi wannan bukata ba shi ba.

"Ina hankali a ce za a gudanar da zabe cikin hanzari idan akwai kati miliyan talatin a hannun INEC wannan shi ne matsayina".

Sauti da bidiyo akan labarin