Buhari zai tattauna da Boko Haram | Siyasa | DW | 29.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari zai tattauna da Boko Haram

Najeriya ta dau sabon salon warware rikicin Boko Haram domin tattauna musanyar kwamndojin kungiyar da 'yan matan makarantan Chibok.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A baya dai an gaza cimma duk wani shirin wata tattaunawa da Kungiyar ta Boko Haram,to sai dai kuma wani Bidiyo a bangare na kungiyar da aka bayyana na neman sauyin lamura tare da neman mahumtan Abuja su amince da musanyar 'yan matan a bisa kowane sharadi.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce mahukuntan kasar na shirin amfani da duk kafofin tattaunawa da suka hada da kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu da nufin musanyar kwamndojin Kungiyar Boko Haram da ke tsare a wasu gidajen yarin kasar domin karbo 'yan matan makarantar Chibok da suka share sama da shekaru biyu a hannun kungiyar. Malam Garba Shehu shi ne kakakin gwamnatin Najeriya ya ce:

"Gwamnati ba ta da haufin zama teburin sulhu da kungiyar, da ma sauran wadanda ke da hanyar shiga tsakani dan tattauna abin da ya da ce."

To sai dai a baya an sha kaiwa ga karatu na damfara tare da karbe kudaden mahukunta a da sunan tattaunawa dama bukatar ceto yan matan amma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu. A baya dai kungiyar ta kai ga fitar da wani bidiyo da ta ambato sunan Ahmed Salkida a matsayin mutumin da kungiyar ta kai ga amincewa ga duk wani sulhu da kila ma ceto 'yan matan. To sai dai kuma tattaunawa da Salkidan a can baya ta kare tare da gaza kaiwa ga biyan bukatu. Wani tsoro kuma a cikin sabon tayi na musanyan na zaman karewa ya zuwa karin karfi ga kungiyar da tuni tai rauni kuma ke magagin mutuwa ya zuwa yanzu. A yanzu dai abin jira a gani dai na zaman tasiri na sabon ta yi da ke iya kaiwa ga kulla amana a tsakanin tsofaffin manyan abokan gabar yakin.

Sauti da bidiyo akan labarin