1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Samar da dokar damawa da matasa a mulki

May 29, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa matasan Najeriya alkawarin samar da wata doka da za ta bai wa matasan kasar damar neman mulki ba tare da fuskantar haramcin karancin shekaru ba.

https://p.dw.com/p/2yX5A
Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Hoto: picture-alliance/dpa

A Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da shirin saka hannu a kan kudurin doka da majalisa ta amince da ita wadda za ta ba matasan kasar damar taka rawa a harakokin siyasar kasar a nan gaba ba tare da fuskantar wani tarnaki ba saboda karancin shekaru. Shugaban ya ambata hakan ne a cikin wani jawabi da ya yi ga 'yan kasar albarkacin ranar zagayowar cikar Najeriya shekaru 19 da komawa turbar demokradiyya.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Anhänger Jubel
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

An dai dauki lokaci ana fafutikar da nufin cika burin a matasan da ke zaman mafi yawa cikin kasar amma kuma 'yan kallo a cikin harkokin mulki sakamakon kayyade shekaru a bangare na dokar zabe ta kasar. To sai dai kuma shugaban da ke biki na cika shekaru uku a bisa mulki ya dau dama domin zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu yayin mulkin. Jawabin na mintuna 25 dai ya tabo batutuwa da daman gaske kama daga batun rashin tsaro ya zuwa yakin hanci da ma kokari na sake farfado da tattali na arzikin Tarrayar Najeriyar kuma a gaba daya a fada ta Buharin an yi nasara a kokari na daukar saiti na kasar ya zuwa tudun mun tsira.


To sai dai kuma in har gwamnatin kasar ta na bugun kirjin yin nasara a kokari na rage barayi cikin kasar a fadar Shehu Musa da ke zaman sakataren jam’iyyar SDP ta adawa matakin gwamnatin kasar bai wuci tozarta 'yan kasar da ke da mugun hatsari a ciki dama wajen tarrayar Najeriyar ba. To sai dai kuma babbar matsalar da ke gaban kasar a halin yanzu na zaman rashin tsaron da ya mammaye sassa da yawa. Kama daga yaki na ta’addancin da ke tashi da lafawa, ya zuwa rikicin makiyaya da manoman da ya hargitsa daukacin tsakiyar Najeriya da ma 'yan ina da kisan da ke cin karensu babu babbaka a jihohi na Arewa maso Yamma, ta yi baki ta kuma lalace ga zaman lafiya da kwanciya ta hankali a halin yanzu.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Anhänger Jubel
Hoto: picture-alliance/AP/J. Delay

To sai dai kuma a fadar kakaki na gwamnatin kasar Mallam garba Shehu, Buharin ya yi nisa da nufin tunkarar matsalar da ke barazana ga daukacin makoma ta kasar. An dai shiga zango na hudu kuma na karshe ga gwamnatin 'yan sauyin da ke fatan komawa zabe da nufin cika burin mai wahala.