1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: An yi Allah wadarai da kisan dalioba a Sokoto

Abdoulaye Mamane Amadou
May 13, 2022

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadarai da kisan dalibar makarantar nan ta Kwalejin ilimi ta Shehu Shagari ta jihar Sokoto da wasu dalibai suka yi, bisa zarginta da yin batanci ga Annabi.

https://p.dw.com/p/4BHc1
Nigerias Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: Julien de Rosa/ Pool/REUTERS

Ita dai daliba Deborah Samuel, ta fuskanci bugu da jifa da duwatsu daga dandazon daliban makarantar, kana daga bisani suka kone gawarta bayan da ta mutu. A wata sanarwar da ya fitar shugaban na Najeriya kasar da ta fi kowace a nahiyar Afirka yawan al'umma, ya ce ba wani dan kasar da ya isa ya yiwa kansa shari'a.

Kafin kiran na shugaban Najeriya shi ma mai alfarma sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar ya bukaci mutanen yankin da su zauna lafiya, bayan da yayi Allah wadarai da kisan dalibar.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin 'yan sanda a wannan jihar da ke kan turbar kwarya-kwaryar shari'ar Muslunci, sun ce sun kama akalla mutun da ake zargi na da hannu wajen tayar da fitinar, kana nan ba da jimawa ba ana shirin gurfara da su a gaban kotu.