Buhari ya sallami Babachir | Labarai | DW | 30.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya sallami Babachir

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sallami Sakataren Gwamnatin kasar Babachir David Lawal daga aiki, ya kuma maye shi da Mr. Boss Mustapha.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami Sakataren Gwamnatin kasar Babachir David Lawal daga aiki, ya kuma maye shi da Mr. Boss Mustapha.

A cewar wata sanarwar da Femi Adesina, mai ba shugaban shawara kan harkokin watsa labarai ya fitar, na cewa shugaba Buhari ya kuma sallami shugaban hukumar tattara bayanan sirrin kasar Ambassador Ayo Oke.

Sanarwar ta ce shugaban kasar ya ce matakin ya bi amfani ne da shawarin da kwamitin da ya binciki manyan jami’an da aka zarga da almundahana ya bayar a baya. Manyan jami’an dai sun musanta zarge-zargen da aka yi masu.

Kafin wannan lokacin dai ‘yan Najeriya da dama sun yi ta sukar gwamnatin kasar da jan kafa wajen daukar matakin da ya dace kann wadannan jami’an. Haka nan wasu 'yan kasar na aza ayar tambaya kan tafiyar gwamnati, musamman ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa da ake ganin shugaba Buhari ne gwanin iya yin hakan