1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya ya bukaci hadin kai

June 15, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci 'yan kasar su manta da bangaranci da banbancin addini, inda ya ce hadin kai da kaunar juna su ne za su kai kasar ga samun ci gaba.

https://p.dw.com/p/2ze8r
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaba Buhari ya gana da shugabannin addinai na Musulunci da Kirista a fadarsa da ke Abuja, wadanda suka je domin taya shi murnar sallah bayan kammala azumin watan Ramadana, inda suka tattauna kan batutuwa da suka shafi zaman lafiya da hadin kan kasa. Shugaban kasar ya shaidawa mahalarta taron cewar ba mafita a tsakanin al’umma kasar idan har ana bukatar ci-gaban kasar face zama wuri guda domin ceto ta daga halin da take ciki a yanzu.

“Bari na jaddada abun da na fada shekaru sama da 30  baya, ba mu da wata kasa face Najeriya saboda haka, gara mu zauna mu hada kai domin ci-gaban kasarmu, ba mu da zabi. Ina gode muku sosai kuma ina son ku je ku shaidawa magoya bayanku su kara aiki tukuru domin kasarmu tare da kaucewa daga batun ni kadai ko kuma 'yan yankinmu”

Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria
Hoto: Reuters/A.Akinleye

Kama daga su kansu talakawa da ma shugabannin da ke jan ragamar harkokin kasar, babbar matsala a cikin Tarrayar Najeriyar na zama banbancin addini da kabila.

Matsalar ta yi nisa har a kungiyoyin addinai na kasar da sannu a hankali suke neman rikidewa ya zuwa kakaki na siyasa.

Reverand Jonah Samson shugaban kungiyar kiristoci na Tarrayar Najeriyar reshen Abuja, ya ce akwai bukatar sauya tunani ga yadda mabiya addinai ke kallon shugabanci a kasar. To sai dai kuma ga su kansu ‘yan kasar da ke fuskantar zabe, a fadar Farfesa Shehu Galadanci da ke zaman babban limamin Abuja, watan Ramadana babban darasi ne ga al’ummar kasar. Gaskiya tsakanin kowa, ko bayan halayya ita kanta barazanar tsaron kasar na rikidewa daga banbancin kabila ya zuwa dan kawu da goggo  fadar ministan tsaron Janar Mansur dan Ali abun kuma da ke tayar da hankalin mahukuntan kasar yanzu.