1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ba zai halarci taron kolin AU ba

March 19, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce sai ya tuntubi kungiyoyin kwadago don sanin matakin da zai dauka kan rawar da kasar za ta taka dangane da yarjejeniyar kasuwancin bai daya a tsakanin kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2ua8D
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Soke halartar taron da ake soma yi a kasar Ruwanda da shugaban Buhari ya yi, ya ja hankulan jama'a musanman masu masana'antu da 'yan kasuwa kan illar janyewa daga taron da ake ganin zai yi matukar tasiri a kokarin da ake na bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Duk da cewar an kira damar karin tattaunawa da Buhari ya bukaci ya yi da kungiyoyin kwadago a matsayin babbar hujjar janyewar Najeriya daga rattaba hannu a bisa yarjejeniyar ciniki na bai daya a kasashen nahiyar Afirka.

Najeriya za ta aika da tawaga zuwa taron na birnin Kigali, janyewar Najeriya da ake yi wa kallon jigo ga kokari na gamayya a tsakanin kasashen Afirkan dai na zaman gagarumin koma baya a cikin yarjejeniyar. Kungiyar kasashen AU na kallon yarjejeniyar a matsayin damar habakka ciniki a tsakanin juna.

Tuni kungiyar kwadago Najeriya ta NLC ta gargadi mahukuntan na Abuja da kada su kuskura su rattaba hannu a bisa yarjejeniyar da a cewarsu ke zaman mai hatsari ga makomar kasar. Ko bayan batun makamashi, babbar matsala ga kasuwar Najeriya a halin yanzu na zaman kwararar kayayyakin waje kama daga shinkafa ya zuwa nama har da man girki da ko bayan barazana ga lafiya ke kuma karya farashi ga kayayyakin gidan da farashin ke neman tashi.