1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May ta bukaci EU ta daga mata kafa

Abdullahi Tanko Bala
March 21, 2019

Firaministar Birtaniya Theresa May za ta sake komawa Hedikwatar Turai a Brussels domin rokon shugabannin tarayyar Turan  su kara mata wa'adin watanni uku akan lokacin da aka tsara na ficewar kasar daga EU.

https://p.dw.com/p/3FQ4x
Großbritanien | Theresa May | Brexit
Hoto: Reuters/Pool/J. Brady

Sau biyu dai yan majalisar dokokin Birtaniyar suna yin watsi da yarjejeniyar da Firaminista May ta cimma da Kungiyar Tarayyar Turai EU.

Da ta ke jawabi Theresa May ta ce a shirye ta ke ta ga an cimma yarjejeniya kan ficewar kasar.

"Ta ce lokaci yayi da za mu cimma matsaya. Kawo yanzu majalisar dokoki ta yi bakin iyawarta domin kaucewa abin da ba'a bukata. Kudiri kan kudiri da kuma kwaskwarima bayan kwaskwarima amma ba tare da majalisa ta yanke hukunci akan abin da ta ke bukata ba. Ina fata 'yan majalisa za su goyi bayan yarjejeniyar da na cimma da kungiyar tarayyar Turai."

A wannan Alhamis din Majalisar dokokin tarayyar Turai za ta gudanar da taro da sauran kasashe 27 na kungiyar ta EU domin sauraron dalilan da Firaministar Birtaniyar Theresa May za ta gabatar na neman jinkirta wa'adin ficewar kasar daga EU.