1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: May za ta sake tattaunawa da shugabannin EU

Abdul-raheem Hassan
January 21, 2019

Mrs May ta jaddada bukatar komawa Brussels karo na biyu domin tattaunawa da shugabannin Tarayyar Turai kan sauye-sauyen da ta amince da su tun farko kan ficewar Birtaniya daga kungiyar a watan jiya.

https://p.dw.com/p/3BvXt
Großbritannien House of Commons in London | Theresa May, Premierministerin
Hoto: picture-alliance/House of Commons/empics

Duk da rashin tasirin Firaministar Birtaniya Theresa May kan daftarin ficewar Birataniya daga EU a majalisar dokokin Birtaniya a makon jiya, amma ta ce ba gudu ba ja da baya kan kudurin ficewar kasar daga EU.

"Da farko akwai alamar yuwar ballewar biratbiya daga kungiyar tarayyar Turai ba tare da wata yarjejeniya ba. Kuma bisa ga dukkan alamu dukkannin bangaorin majalisa na son gwamnati ta cimma wannan mastaya. To amma yakamata mu gayawa kanmu gaskiya mu fayyacewa jama'a a abinda hakan ke nufi. Hanya mafi dacewa na cimma hakan ba tare yarjejeniya ba shi ne majalisa ta amince da yarjejeniya tare da kungiyar EU. Wannan shi ne gwamnati ke fata.