1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkirta fitar Birtaniya daga EU

Ramatu Garba Baba LMJ
September 4, 2019

Jam’iyyar da ke mulki a Birtaniya da 'yan adawa sun taka birki ga gwamnatin kasar, a zaben da ta sha kaye a mataki na farko na fafutukar hana Birtaniya ficewa daga cikin kungiyar EU ba tare da yarjejeniya ba.

https://p.dw.com/p/3OztD
Großbritannien Brexit | House of Commons, Unterhaus | Boris Johnson, Premierminister
Firaministan Birtaniya Boris JohnsonHoto: picture-alliance/Xinhua/UK Parliament/R. Harris

Bayan rikita-rikitar siyasa ta tsawon kwanaki a Birtaniya dangane da kammala ficewar kasar daga cikin Tarayyar Turai ba tare da an cimma yarjejeniya ba, 'yan majalisun dokoki na jam'iyyar Conservative mai mulkin kasar da na bangaren adawa, sun kayar da gwamnati a kokarin da suke na hana kasar ficewa daga EU ba tare da yarjejeniya ba. Majalisar dai ta gudanar da zabe inda masu goyon bayan ta karbe ikon gudanarwa suka yi nasarar kayar da masu goyon bayan Firaminista Johnson da kuri'u 328 shi kuma ya sami 301. Sai dai Firaiminista Boris Johnson ya sha alwashin daukar mataki, inda ya yi alkawarin gabatar da wani kuduri da zai bayar da izinin gudanar da zaben gama gari.

A daya bangaren kuwa, jagoran jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya nemi majalisar da ta gaggauta gabatar da kudurin hana Birtaniya ficewa daga Tarayyar Turai kafin a gudanar da zaben, sannan da kakausar murya a ya fito karara yana mai cewa:

Großbritannien London | Jeremy Corbyn im britischen Unterhaus antwortet auf Boris Johnson Ansprache
Jeremy Corbyn jagoran jam'iyyar adawa ta Labour a BirtaniyaHoto: picture-alliance/empics/House of Commons

''Firaiminsitan ya yi ikirarin samun ci gaba a tattaunawa da kungiyar EU, amma mun san ba haka bane. Baro-baro mun ga gangancin da wannan gwamnatin ke yi. Ba ta da niyya face taga ta yanke kauna da EU ba tare da cimma yarejejeniya ba. Wannan na nufin karancin abinci da magunguna da hargitsi a iyakokin kasar. A bayyane hakan yaake cikin wasu bayanan sirri da aka bankado.''

Da wannan sakamako dai, za su iya gabatar da kudurin doka da zai jinkirta ranar ficewar Birtaniyan daga Tarayyar ta Turai wanda, a baya aka tsara yi a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa. A yanzu dai ana sa ran 'yan majalisar za su gabatar da kudirin da zai nemi dage batun kammala ficewar Birtaniyan zuwa 31 ga watan Janairun shekara ta 2020 da ke tafe.