Boren adawa da taron AFD mai kyamar baki | Labarai | DW | 02.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren adawa da taron AFD mai kyamar baki

Jami'in dan sanda da mutum guda ne suka samu raunuka, a lokacin wani boren adawa da taron jam'iyyar masu kyamar baki ta AFD wanda ya rikide zuwa tarzoma a birnin Hannover da ke yankin arewacin Tarayyar Jamus.

Mai magana da yawun 'yan sanda ta shaidar da cewar an yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa daruruwan masu zanga zangar, wadanda suka tattare tituna da hanyoyin shiga inda ake taron jam'iyyar ta AFD.

Ta ce wani jami'in dan sanda ya samu rauni a hannu, sakamakon jifansa da kwalba da daya daga cikin masu zanga zangar yayi, ka na wani da yanzu ke kwance a asibi ya samu karaya a kafarsa.

 Sai dai duk da barkewar tarzomar taron jam'iyyar AFD na cigaba da gudana, wanda akesaran zai mayar da hankali wajen shawo kan matsaloli na cikin gida na rarrabuwar kawuna tsakanin magoya bayanta .

Jam'iyar mai akidar kyamar baki dai ta samu tagomashi a zaben kasa da ya gudana a watan Satumba, nasarar da aka danganta da adawa da akidar shugabar gwamnati Angela Merkel na bude kofofin Jamus wa baki 'yan gudun hijira.