Bom ya yi sanadiyyar hadarin jirgin Rasha? | Labarai | DW | 06.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bom ya yi sanadiyyar hadarin jirgin Rasha?

Wasu bayanan sirri da jami'an leken asirin Amirka da Birtaniya suka samu ta hanyar tauraren dan Adam na nuni da cewa akwai alamun bom a faduwar jirgin Rasha a Masar

Wasu bayanan sirri da jami'an leken asirin Amirka da Birtaniya suka samu a cikin wata hira da mambobin Kungiyar IS na Siriya da Masar su ka nado ta hanyoyin sadarwa na zamani sun nunar da cewa akwai alamun da ke nuni da cewa an saka bom a cikin jirgin kasar Rashar nan da ya fadi a yankin Sinai na Masar a ranar Asabar da ta gabata.

Jaridar Birtaniya ta The Times wacce ta ruwaito wannan labari a wannan Jumma'a ta ce bayanan firar da aka nada da kuma yanda hira ta gudana sun bai wa masu bincike kwarin gwywar cewa wani fasinjan jirgin ko kuma wani ma'aikacin filin jirgi ya saka bom a cikin jirgin.

Sai dai wani jami'in da ke magana da yawun firaministan Birtaniya David Cameron ya ki ya tabbatar da labarin wanda ya ce a halin yanzu batu ne da ya shafi leken asiri. .