Boko Haram: Yara miliyan daya ba sa karatu | Labarai | DW | 22.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram: Yara miliyan daya ba sa karatu

Rikicin Boko Haram da wasu kasashe a yammacin Afirka ke fama da shi musamman Najeriya ya hana yara kimanin miliyan guda zuwa makaranta.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rashin zuwa makaranta da yara ke yi a arewacin Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram ka iya taimakawa wajen haifar da karin masu tsaurin kishin addini.

Asusun dai ya bayyana hakan ne a wani sabon rahoto da ya fidda kuma hakan inji jami'in da ke kula da asusun a yammaci da tsakiyar Afirka Manuel Fontaine in yaran ba sa zuwa makarata, 'yan ta'adda ka iya sace su sannan su sanyasu a turbar da ba ta dace ba.

Kimanin makarantu 2000 ne wannan rikici ya sanya aka rufe su a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, yayin da dalibai sama da miliyan guda ba sa zuwa makaranta kana daruruwan malamai suka rasa ransu sakamakon rikicin.

Hukumomi a Najeriya dai sun lashi takobin kawo karshen tada kayar baya ta kungiyar ta Boko Haram a Najeriya. Rikicin dai ya yi sanadin rasuwar dubban mutane.