Boko Haram ta sako malaman jami′a da ta tsare | Labarai | DW | 11.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sako malaman jami'a da ta tsare

Mayakan Boko Haram sun saki wasu mutane13 da suka yi garkuwa da su a Najeriya kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana a ranar Asabar.

Malaman jami'a uku da aka kama a shekarar bara na cikin wadanda a ka saki tare da wasu mata guda goma wadanda suka kasance matan 'yan sanda kamar yadda Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban ya bayyana.

An dai kai ga cimma yarjejeniyar sakin wadannan mutane bisa sanya bakin kungiyar aikin agaji ta kasa da kasa wato Red Cross. Mai magana da yawun shugaban na Najeriya dai bai yi karin haske ba ko an biya kudin fansa kafin sakin wadannan mutane 13 da aka yi garkuwan da su.

Wadannan malamai na jami'ar Maiduguri an kama su lokacin da suka je wani aiki da ya shafi hakar mai a yankin Tafkin Chadi, yayin da matan 'yan sandan kuma aka kama su lokacin wata jana'iza a yankin na Borno arewa maso gabashin Najeriya.