Boko Haram ta sake kai hari a garin Gamboru na jihar Borno | Labarai | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sake kai hari a garin Gamboru na jihar Borno

Akalla mutane takwas sun rasa rayukansu a harin 'yan bindiga a Gamboru da ya biyo bayan kwato garin da sojoji suka yi.

Wani sabon hari da wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai ya yi sanadiyyar rayukan mutane takwas wasu da dama kuma suka jikata a garin Gamboru da ke jihar Borno a Najeriya. Wani da ya tsira daga harin kuma ya shiga yankin kasar Kamaru ya shaida wa wakilinmu a Gombe Al-Amin Suleiman Mohammed ta wayar tarho cewa tun a ranar Laraba 'yan bindigar suka afka wa garin inda suka tarar da mutanen da ke komawa suna kwashe sauran kayansu bayan da dakarun kawance suka karbo garin daga mayakan Boko Haram.

Ko da safiyar wannan Alhamis ma rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun sake hallaka wasu mutanen garin, sai dai ba a samu yawan alkaluma na wadanda abin ya rutsa da su ba.