Boko Haram ta sake hallaka mutane a Najeriya | Labarai | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sake hallaka mutane a Najeriya

Shaidu arewa maso gabashi Najeriya sun ce mayaka Boko Haram sun kashe mutane 18.

Masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram a kan babura sun kashe akalla mutane 18 a wani hari da suka kai a garin Shaffa da ke arewa maso gabashin Najeriya. Wadanda suka shaida lamarin su fada a wannan Alhamis cewa an kai harin ne a daren ranar Laraba, inda aka bar gawarwakin mutane yashe a kan titi, kamar yadda Amos Msheli wanda ya tsira da ransa bayan ya shiga cikin wani daji da ke kusa sannan ya tsere zuwa garin Biu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Reuters. Hakan dai na zuwa ne bayan rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe mutumin da ke amsa sunan Abubakar Shekau da ke zama jagoran kungiyar ta Boko Haram, bayan wata musayar wuta a tsakiyar wannan wata na Satumba.