Boko Haram ta sace mutane 100 | Labarai | DW | 15.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta sace mutane 100

A Tarayyar Najeriya wasu gungun mutane dauke da makamai sun sace sama da maza yara da manya masu yawa.

Rahotanni daga tarayyar ta Najeriya na nuni da cewa wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke gwagwarmaya da makamai a kasar sun sace mutane masu yawa a arewa maso gabashin kasar. Wannan al'amari dai ya faru ne bayan da maharan dauke da makamai suka kai farmaki wani kauye tare da loda mutanen da suka sace da dukansu maza yara da manya sama da 100 a manyan motaci suka kuma fice da su daga jihar. Dama dai batun sace mutane a wannan yankin ba wani bakon abu bane domin koda a watanni hudu da suka gabata ma sai da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace wasu 'yan mata 'yan makarantar Sakandare sama da 200 a garin Cibok dake jihar Borno.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu