1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mata 14 kan zargin maita

Ramatu Garba Baba
November 14, 2022

Ana zargin wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram da laifin hannu a kashe wasu mata da ya zarga da laifin maita a jihar Bornon Najeriya.

https://p.dw.com/p/4JW56
Hoto: Maxwell Suuk/DW

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun hallaka wasu gomman mata da suka dora wa alhakin hallaka 'ya'yan shugabansu ta hanyar maita a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar. 

Talkwe Linbe da ta tsira daga hannun Boko Haram ce ta sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP, yadda babban kwamandan kungiyar mai suna Ali Guyile ya fusata da mutuwar baka-tatan na 'ya'yansa a lokaci guda.

Madam Linbe ta ce, Guyile ya bayar da umarnin kamo duk matan yankin da ake zargi da maita kafin daga bisani ya sa aka yi wa goma sha hudu daga cikinsu yankan rago. Lamarin ya faru ne a garin Gwoza da ke jihar Bornon a ranar Alhamis da ta gabata sai dai kawo yanzu mahukuntan jihar ba su iya tabbatar da labarin ba.