Najeriya: Boko Haram ta kashe sojoji 48
September 3, 2018Rahotannin farko sun ce mayakan mayakan Boko haram sun kashe sojoji 30 a loakcin da kungiyarsu ta yi wa sojojin kofar rago a wani yanki da ke jihar Borno mai iyaka da Nijar a ranar Alhamis da ta gabata. A yanzu dai adadin sojojin 48 mayakan suka kashe, yayin da wasu rahotanni ke cewa an halaka 'yan Boko Haram da dama.
Wata sanarwa da rundunar tsaron Najeriyar ta fitar bayan harin, na cewa dakarun sun yi musanyar wuta da mayakan na Boko Haram. Sannan ta musanta yawan sojojin da Boko Haran ta yi ikirarin halakawa.
Wannan ba shi ne karon farko da kungiyar Boko Haram ke kaddamar da hare-hare kan sansanin sojojin Najeriyar ba, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ikirarin karya lagon kungiyar da ke barazana ga rayuwar jami'an tsaro da fararen hula.
Sai dai yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriyar NAN kakakin rundunar sojin kasar ya musanta rahotannin da ke cewa mayakan sun kashe sojoji 48.