Boko Haram ta kashe mutane 65 a Borno | Labarai | DW | 29.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kashe mutane 65 a Borno

Maharan a kan babura da motoci sun bude wuta ne kan mutanen da ke dawowa daga jana'iza kuma harin ya jikkata wasu da dama. Wannan dai shi ne hari mafi muni kan fararen hula a baya-bayannan.

Akalla mutane 65 ne aka tabbatar da mutuwarsu a sabon harin da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kaddamar a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin sai dai mayakan Boko Haram sun sha kai makamancin wannan mumunan hari kan fararen hula da jami'an tsaron Najeriya. Harin ya zo ne a lokacin da ake cika shekaru da fara rikicin Boko Haram a kasar. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin.