1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram na zafafa hari kan manoma

Abdul-raheem Hassan MNA
November 20, 2018

'Yan bindiga sun kashe manoma tara tare da yin garkuwa da mutane 12 bayan da suka bude wuta a gonaki da ke kauyukan jihar Borno.

https://p.dw.com/p/38aia
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Wasu shedu sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa mayakan sun shiga kauyen Mammanti, inda suka bude wuta kan manoma da ke ayyuka a gonakinsu.

Babu dai martani daga bangaren jami'an tsaron Najeriya kan sabon harin, amma a baya-bayan nan mayakan Boko Haram na zafafa hare-hare kan mazauna garin Mammanti tare da kashe mutane da satar shanu.

Wasu majiyooi na zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da hare-hare kan manoman a matsayin daukar fansa kan yadda suke fallasa maboyarsu ga jami'an tsaro.

Sama da mutane dubu 27 ne rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar rayukansu, sama da mutane miliyan daya da rabi na gudun hijira tun fara rikicin a shekarar 2009.