Boko Haram ta kai farmaki makarantar ′yan mata a jihar Yobe | Labarai | DW | 20.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta kai farmaki makarantar 'yan mata a jihar Yobe

Masu ikirarin jihadin na Boko Haram sun kai farmaki makarantar 'yan mata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya lamarin da ya haifar da fargaba.

Boko Haram (Java)

An dai shiga kwan gaba kwan baya kan matsalar ta Boko Haram a Najeriyar

Mayakan da suka ja wata tawaga cikin motoci samfurin akori kura ta daukar kaya sun isa kauyen Dapchi a yankin Bursari na jihar Yobe da misalin karfe shida na yammaci inda suka tunkari makarantar kamar yadda Sheriff Aisami wani da ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Aisami ya ce da saukar mayakan a garin sun rika harbe-harbe da fasa wasu abubuwa masu kara, wannan ya ja hankalin 'yan makarantar ta 'yan mata da ke garin inda daliban da malamansu suka ranta cikin na kare kafin mayakan su karasa makarantar. 'Yan kungiyar dai ta Boko Haram sun sace kayayyaki da suke bukata a makarantar.