Najeriya: Boko Haram ta kai hari a Kondiga
July 31, 2019Talla
Mayakan Kungiyar Boko Haram sun hallaka wasu mutane biyu tare jikkata wasu jama’a da dama a wani harin da su kai a kauye Jakana da ke karamar hukumar Konduga mai tazarar kilomita 40 daga Maiduguri a Arewa maso Gabashin Najeriya. Rahotanni daga yankin sun ce mayakan sun kuma sace mutane ciki har da mata da matasa tare da kwasar kayan abinci da kona gidaje da shagunan jama’a da wasu kaddarorin gwamnati. Wani daga cikin masu aiyukan jinkai a yakin Malam Abdul’aziz Mala ya bayyana wa wakilinmu na yankin cewa jama’a na cikin fargaba. Kungiyar Boko Haram dai ta kara zafafa hare-harenta a ‘yan kwanakin nan inda ko a karshen makon da ya gabata mayakan suka hallaka mutane sama da 60 a Jihar ta Borno da ke Arewa maso Gabashin Kasar.