Boko Haram ta halaka mutane a Borno | Labarai | DW | 23.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta halaka mutane a Borno

Ana zargin dai mayakan na Boko Haram su tara sun shiga kauyen Kijimatari, da ke Arewa maso Gabashi na jihar Borno cikin dare inda suka shiga gidaje wasu mutane shida da halakasu.

A daren Litinin wayewar garin Talata mayakan Boko Haram sun kashe wasu mutane shida a wani kauye da ke a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya a wani hari da ake ganin tsararre ne don halaka wasu mutane kamar yadda 'yan kato da gora suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Ana zargin dai mayakan na Boko Haram su tara sun shiga kauyen Kijimatari, da ke Arewa maso Gabashi na jihar Borno cikin dare inda suka shiga gidaje wasu mutane shida da halakasu ciki kuwa harda shugaban al'ummar kauyen.

A cewar Ibrahim Liman da ke zama shugaban 'yan kato da gora a yankin mayakan sun kaucewa shingaye bincike na soja inda suka shiga kauyen ta daji suka shiga garin ta baya. Shi ma Kulo Musa wani mazaunin garin ya ce mayakan sun zabi amfani da wukake wajen yanka wadanda suka kaiwa harin sabanin amfani da bindiga da kararta za ta iya jan hankali na jami'an tsaro da ke aikin kula da shingen bincike.