Boko Haram ta afkawa wani kauye | Labarai | DW | 13.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta afkawa wani kauye

Labarin da muke samu daga Najeriya na cewar 'yan kungiyar nan ta Boko Haram sun hallaka mutane hudu tare da kone gidaje da dama a kauyen Amarwa da ke da tazarar kilomita 20 da birnin Maiduguri fadar jihar Borno.

Masu aiko da rahotanni suka ce 'yan Boko Haram din sun shiga kauyen ne da misalin karfe 11 na daren jiya Asabar idan suka kama yin harbi irin na kan mai uwa da wabi kafin daga bisani kuma suka fara cinnawa gidajen mutane wuta. Wani basaraken a garin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar biyu daga cikin wanda aka kashe sun rasu ne sakamakon harbin bindiga yayin da saura biyu suka rasu a wasu daga cikin gidajen da aka kone. A watan Mayun da ya gabata ma dai wannan kauye na Amarwa ya fuskanci harin 'yan Boko Haram wanda suka yi wa kauyen tsinke a kan babura kana suka harbe wasu manoma shidda har lahira a lokacin da suke yin shuka.