1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram sun kashe 'yan Chadi

July 24, 2018

Mayakan kungiyar Boko Haram sun halaka wasu manoma 18 tare da yin awon gaba da wasu mata su tara a yammacin kasar Chadi.

https://p.dw.com/p/31yVv
Boko Haram
Hoto: Java

Hukumomi a kasar Chadi, sun ce wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun halaka wasu manoma 18 tare da yin awon gaba da wasu mata su tara a yankin yammacin kasar.

Shaidu sun ce maharan sun afka wa kauyen Mayerom ne da ke yammacin Chadin a ranar Alhamis na makon jiya, suka kuma yi wa mutanen 18 yankan rago, sai dai an ce akwai wata matar da ta tsere.

Wasu bayanan na cewa manoman sun wuce iyakar da jami'an tsaro suka amince su rika noma a ciki, abin da wasu da dama ke ganin shi ne ya sanya su shiga wannan hadari.

Kasar ta Chadi dai bata fuskanci tsananin hare-hare daga kungiyar Boko Haram ba, idan aka kwatanta da makobtan kasashe irinsu Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.